Mazauna babban birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa da kyar suke samun na abinci saboda tsadar rayuwar da ake ciki.
Hakanan sun kuma koka da tsadar kudin ababen bayan wanda hakan ya biyo bayan kara farashin litar man fetur ne da aka yi.
Mutanen sun zanta da kamfanin dillancin labaran Najeriya ne NAN inda suke kokawa da irin halin matsin rayuwar da suke ciki.
Sun yi roko ga gwamnatoci a kowane mataki dasu dauki matakan ragewa al’umma radadin rayuwa da suke ciki.