
Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ya shirya yin wa’adin shekara huɗu kacal idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Obi, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir el-Rufai, na shirya kafa kawance domin ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027.
Da yake magana a wata tattaunawa ta “Twitter Space” da Parallel Facts suka shirya a ranar Lahadi, Obi ya ce duk wani ɗan takara daga kudancin Najeriya da aka zaɓa shugaban ƙasa a 2027 dole ya kasance cikin shiri ya sauka daga mulki ranar 28 ga Mayu, 2031, bisa abin da ya kira “yarjejeniya marar rubutu” da kuma tsarin rabon mulki.
Ya ƙara da cewa tsarin rabon mulki — wanda ke ba da damar mulki ya rika zagaya tsakanin arewa da kudu — wani abu ne da ya daɗe yana goyon baya.
Idan wannan kawance ya ba shi tikitin tsayawa takara a 2027 bisa wannan yarjejeniya ta fahimtar juna, kuma idan ya yi nasara, Obi ya ce ba zai ƙara wata rana a kan wa’adin mulki ba.