Shahararren dan daudu, Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky ya samu fita daga Najeriya kwanaki kadan bayan da aka kamashi amma aka bayar da belinsa.
Ana dai zargin Bobrisky da laifin rashawa da cin hanci ne
Bobrisky ya bayyana fitarsa daga Najeriya ne zuwa kasar waje ta hanyar shafinsa na sada zumunta saidai bai fadi kasar da ya tafi ba.
Yace Naira Miliyan 30 ya kashe wajan siyan tikitin jirgin First Class.
A baya dai an ga yanda aka kama Bobrisky aka fitar dashi daga cikin jirgi da karfin tsiya a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Birnin Landan na kasar Ingila.
Daga baya ta bayyana cewa hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ce ta kamashi.
Daga baya an daukeshi daga Legas zuwa Abuja. Kuma hukumar ta EFCC ta bayyana cewa ta kamashine saboda yaki amsa gayyatar da aka masa.
Hukumar ta EFCC ta bayar da belinsa bayan da ya musanta zargin rashawa da cin hancin da ake masa.