Rikicin cikin gida na jam’iyyar NNPP na kara kazanta bayan sa rahotanni suka bayyana cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yaki daukar wayar Kwankwaso bayan da ya kirashi kuma yaki halartar taron ganawa da Kwankwason.
Sarar Abba Tsaya da kafarka wadda ke nufin Abba ya raba gari da Kwankwaso na kara samun yaduwa a siyasar ta Kano.
Jam’iyyar ta rabu gida biyu inda wasu ke son a hada kai da APC a matakin tarayya, wasu kuma sun je kotu suna son a basu iko da shugabancin jam’iyyar dan kwace ragamarta daga hannun Kwankwaso.
Rahoton jaridar Daily Nigerian ya bayyana wanda ke kokarin ganin sun zuga Abba ya bijirewa Kwankwaso kamar haka:
Sakataren Gwamnatin Jihar, Baffa Bichi.
Kwamishinan Tafiye-tafiye, Mohammed Diggol.
Kwamishinan Ilimi, Umar Doguwa.
Sanatan dake wakiltar Kano ta kudu, Kawu Sumaila.
Da kuma Ali Madaki da dai sauransu.
Jaridar tace Gwamnan tuni ya ji hure kunnen da ake masa na ya bijirewa Kwankwaso dan tsayawa da kafarsa.
Rahoton yace wata majiya daga jihar tace Abba yana girmama Kwankwaso saboda har yanzu kaso 90 na kwamishinonin jihar Kwankwasone ya kawosu.
Kuma Abba bai canjasu ba duk da yake cewa wasu basu iya aiki ba ko kuma suna yiwa gwamnan rashin da’a.