A ranar Litinin an samu masu zanga-zanga da yaqa sun je Hedikwatar kamfanin mai na kasa,NNPCL inda suke nema shugaban kamfanin yayi murabus.
Masu zanga-zangar wanda wasu kungiyoyin dake ikirarin kare hakkokin al’umma suka jagoranta sun zargi Shugaban na NNPCL, Abba kyari da rashin iya aiki saboda yanda man fetur ke ta kara tsada.
Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar, Abdullahi Bilal ya bayyana cewa shugabancin kamfanin na NNPCL ya gaza.
Masu zanga-zangar sun kuma nemi a dakatar da shigo da man fetur daga kasar waje inda suka ce yana lalatawa mutane motoci a Najeriya.