Darajar Naira ta fadi a kasuwar canji ta gwamnati a jiya, Alhamis.
Kwanaki 3 kenan a jere darajar Nairar na faduwa a kasuwar Gwamnati.
A jiyan, an sayi dalar Amurka akan Naira N1,484.76 wanda hakan ke nuna Naira ta samu faduwar 145.2 idan aka kwatanta da farashin ranar Laraba na Naira N1329.65 akan kowace dala.
Saidai a kasuwar ‘yan Chanji, Nairar ta dan samu tagomashi na Naira 5, inda aka sayi dalar akan Naira N1,485.