Sanata Barau I. Jibrin yayi alhinin rasuwar daya daga cikin hadimansa me suna Corporal Barde Nuhu da ya rasu a hadarin mota.
Corporal Barde Nuhu ya rasune a yayin da yake kan hanyar zuwa gida jihar Naija dan ganawa da iyalansa.
Yana kan hanyar zuwa Kauyen Shata ne dake karamar hukumar Bosso a jihar ta Naija yayin da hadarin ya rutsa dashi.
Sanata Barau a sanarwar da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ismail Mudashir yace Barde hazikine sosai wajan aiki.
Yace yana mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin da kuma hukumar ‘yansandan Najeriya.