Thursday, December 26
Shadow

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kuɗin sama da naira biliyan 500

A jihar Kano, wacce ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya, gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2025 a gaban majalisar dokokin jihar.

Kasafin kuɗin na bana wanda shi ne na biyu da gwamnan ya gabatar ya kai fiye da naira biliyan 500B.

Duk da kasancewar jihar cibiyar harkokin kasuwanci amma ta na sahun gaba wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, abin da ya sa gwamnati ta ware fiye da kashi 31 na kasafin ga ilimi.

Ma’aikatu da kuɗin da aka ware musu:

  • Ilimi: Naira biliyan 168.4 (kashi 31%)
  • Lafiya: Naira biliyan 90. 6
  • Sufuri: Naira biliyan 12. 2
  • Harkokin noma: Naira biliyan 21.03
  • Albarkatun ruwa: Naira biliyan 27. 23
  • Samar da ababen more rayuwa: Naira biliyan 70.78
Karanta Wannan  Sau nawa ake jima'i: Sau nawa ya kamata ayi jima'i

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *