Sunday, December 22
Shadow

Obaseki ya ce ba ya fargabar binciken EFCC

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ce ya samu labarin cewa EFCC za ta kama shi da zarar ya miƙa mulki a makon gobe.

Sai dai gwamnan ya ce ko kaɗan shi ba ya tsoro ko fargaba domin za a bincike shi a game wa’adin gwamnatinsa, kamar yadda jaridar Thisday ta ruwaito shi yana faɗa a taron EdoBEST da aka yi a Abuja.

“Na samu labarin cewa EFCC za ta kama ni makon gobe. Duk inda suka ajiye ni, zan yi amfani da damar domin gudanar da bincike.

“Mun yi aikace-aikace muhimmai, sannan mun ba mutanen jihar Edo da abubuwan da suka fi buƙata muhimmanci. Don haka me zai sa in yi fargaba? na yi abin da zan iya yi, amma za su iya zuwa su ci gaba da bi-ta-da-ƙullin da za su yi, wannan matsalarsu ce.”

Karanta Wannan  Kalli Hotuna da Bidiyo sun bayyana na wannan dan kasuwar yana lalata da matan manyan mutane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *