Monday, December 9
Shadow

Osinbajo ya baiwa Tinubu shawarar ya tallafawa talakawa dan ana cikin matsi

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar ya tallafawa Talakawa saboda ana cikin matsi.

Osinbajo ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar na mata dake harkar kasuwanci.

Yace Mata kaso 67 wanda mafi yawancinsu suna Arewa ne basu da karfin tattalin arziki kuma hakan na da alaka da rashin Ilimi.

Yace kasar dake da kusan rabin mutanen kasar basu da madogara a rayuwa kuma saboda rashin karfin tattalin arziki akwai matsala.

Dan haka ya baiwa shugaban kasar shawarar fito da wani tsari na tallafawa mutane marasa karfi inda yace ya kuma kamata a baiwa bangaren Ilimi muhimmanci sosai.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo da hotuna yanda motar Dangote ta buge mutane 3 suka mùtù a Jihar Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *