Rahotanni sun bayyana cewa, Matatar man fetur ta Dangote zata fara fitar da man fetur din zuwa kasashen Africa 7.
A yanzu dai matatar ta shirya tsaf dan fara fitar da man fetur din zuwa kasashen South Africa, Angola, da Namibia.
Sannan kuma tana tattaunawa da kasashen Niger Republic, Chad, Burkina Faso da Central Africa Republic dan fara kai musu man fetur din.
Hakana wata majiya tace akwai karin kasashe da ake sa ran zasu bayyana son daukar man fetur din na Dangote.
Misali kasar Ghana ma an bayyana cewa tana son fara magana da Dangote dan fara sayen man fetur dinsa.
Shugaban hukumar kula da man fetur ta kasar Ghana,Mustapha Abdul-Hamid ya bayyana cewa fara siyen man fetur din daga hannun Dangote zai sa su daina sayen man fetur din daga kasashen Turai