Monday, December 9
Shadow

Sabuwar kungiyar dake ikirarin Jìhàdì me suna Làkùràwà ta karbe iko da kananan hukumomi 5 a jihar Sokoto

Sabuwar kungiyar dake ikirarin Jihadi me suna Lakurawa a jihar Sokoto ta karbe iko da wasu bangarori na kananan hukumomi 5 a jihar Sokoto inda take karbar Haraji da Zakka.

Kananan hukumomin da Kungiyar ta kama iko da su sun hada da Tangaza, Gada, Illela, Silame, da Binji kamar yanda wata majiya ta bayyanawa jaridar Vanguard.

Rahoton yace wannan kungiya ta Lakurawa na magana da yarukan Hausa, Fulani, Tuareg, Kanuri, Tuba, da Turanci.

Rahoton yace mutanen na zuwane a babura inda sukan bar wasu su musu gadi sannan su tafi wani garin.

Shugaban karamar hukumar Tangaza, Alhaji Isa Salihu Kalenjeni ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ko da kwanannan sai da suka kwacewa wani dan kasuwa Naira Miliyan 2 sannan suka kwace masa mota sai da ya biya Naira 350,000 sannan suka bar masa ita.

Karanta Wannan  Sojoji Śun Ķashe 'Ýan Ța’àďda 1,166, Yayin Da Suka Kama 1,096, Inji Hedikwatar Tsaro

Me kula da bangaren yada labarai na sojojin Najeriya, Major Gen Edward Buba ya tabbatar da bullar mutanen inda yace suna da alaka da kungiyar ISÌS.

Yace sun yi amfani da iyakar Najeriya da Nijar ce wadda bata da tsaro sosai suke shigowa kasar.

Yayi kira ga duk wanda ya samu bayanai akan kungiyar ya sanar da jami’an tsaro da gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *