Wednesday, May 13
Shadow

Ku daina Rige-Rigen zuwa kasashen waje neman aiki, Ku tsaya mu gyara kasa>>Shugaba Tinibu ya roki Matasa

Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya roki matasan Najeriya da su daina rige-rigen fita kasashen waje neman aiki.

Shugaban ya roki matasa da su tsaya a gyara kasa dan kuwa Najeriya ma zata iya zama kamar kasashen da suke mafarkin zuwa.

Tinubu ya bayyana hakane a wajan taron yaye daliban Jami’ar Uyo inda shugaban jami’ar Port Harcourt, Prof. Owunari Georgewill ya wakilceshi.

Ya jawo hankalin matasan akan su yi amfani da ilimin da suke dashi wajan warware matsalolin da ake dasu a Najeriya.

Karanta Wannan  Wallahi idan Jam'iyyar su Atiku ta karbi mulki sai kun ce gara Tinubu dasu>>Sheikh Musa Asadussunnah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *