Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya roki matasan Najeriya da su daina rige-rigen fita kasashen waje neman aiki.
Shugaban ya roki matasa da su tsaya a gyara kasa dan kuwa Najeriya ma zata iya zama kamar kasashen da suke mafarkin zuwa.
Tinubu ya bayyana hakane a wajan taron yaye daliban Jami’ar Uyo inda shugaban jami’ar Port Harcourt, Prof. Owunari Georgewill ya wakilceshi.
Ya jawo hankalin matasan akan su yi amfani da ilimin da suke dashi wajan warware matsalolin da ake dasu a Najeriya.