Sanata Sani Musa wanda shine shugaban kwamitin dake kula da kudi a majalisar tarayya ya bayyana cewa, cire tallafin man fetur ne abu mafi kyau da ya faru da Najeriya.
Yace hakan zai bayar da damar yanayin kasuwa ya bayyana farashin man fetur din.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace wannan mataki zai bayar da damar raba arzikin gwamnati yanda ya kamata.
Yace idan dai kudaden da ake turawa Gwamnoni suna aiki dasu yanda ya kamata, za’a samu ci gaba sosai.
Yace cire tallafin zai sa gwamnati ta samu karin kudin shiga ta yanda zata rika kashe kudaden nata ta hanyar da ya dace.