Friday, November 14
Shadow

Cire tallafin Man fetur ne abu mafi kyau da armashi da ya faru da Najeriya>>Inji Sanata Sani Musa

Sanata Sani Musa wanda shine shugaban kwamitin dake kula da kudi a majalisar tarayya ya bayyana cewa, cire tallafin man fetur ne abu mafi kyau da ya faru da Najeriya.

Yace hakan zai bayar da damar yanayin kasuwa ya bayyana farashin man fetur din.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace wannan mataki zai bayar da damar raba arzikin gwamnati yanda ya kamata.

Yace idan dai kudaden da ake turawa Gwamnoni suna aiki dasu yanda ya kamata, za’a samu ci gaba sosai.

Yace cire tallafin zai sa gwamnati ta samu karin kudin shiga ta yanda zata rika kashe kudaden nata ta hanyar da ya dace.

Karanta Wannan  Duk rintsi muna tare da Kashim Shettima>>Rahama Sadau bayan dambarwar data faru inda Ganduje ya kira sunan shugaba Tinubu ba tare da kiran sunan Kashim Shettima ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *