Monday, December 16
Shadow

Kotu ta samu Donald Trump da laifukan tuhume-tuhume 34 da ake masa

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya zamo shugaban Amurka na farko da za a yankewa hukunci a kan tuhuma ta mugun laifi, bayan da masu taimaka wa alkali yanke hukunci suka same shi da laifi a tuhume-tuhume 34 da ake yi masa.

Dukkan tuhume-tuhumen na da alaka da karyar da ya yi a harkokin kasuwancinsa domin boye kudin da ya bayar na toshiyar baki a kan alakarsu da mai fitowa a fina-finan batsa wato Stormy Daniels a lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban kasar a 2016.

Da yake Magana a wajen kotun da ke Manhattan bayan samunsa da laifi, Donald Trump, wanda za a yankewa hukunci a watan Yuli mai zuwa, ya kira sakamakon zaman da aka yi a matsayin an yi masa almundahana da coge kuma hakan wani babban aibune.

Karanta Wannan  Kungiyar kwadago ta NLC ta ki amincewa da tayin Naira Dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi, zata shiga yajin aiki

Sannan ya kara da cewa al’umma za su yanke hukunci na gaskiya a ranar zabe mai zuwa a watan Nuwamba.

Tuni dai shugaba Biden ya yi maraba da sakamakon shari’ar ta ranar Alhamis, ya na mai cewa ba wanda ya fi karfin doka.

Kazalika a wata sanarwa da kwamitin yakin neman zabensa ya fitar, ya jaddada cewa, a matsayin mutumin da ake ganin zai yi wa jam’iyyar Republican takara a watan Nuwamba, Donald Trump, zai ci gaba da kasancewa babbar barazana ga dimokradiyya, sannan ya zarge shi da kara kambama aniyarsa ta kullata da neman yin ramuwar gayya.

Sabanin haka, shugaban majalisar wakilai ta Amurka, Mike Johnson, ya kira zaman kotun a matsayin abin kunya da alawadai ga Amurka, sannan ya ce Trump zai daukaka kara.

Karanta Wannan  Mu fa har yanzu muna nan kan matsayin mu sai Gwamnati ta biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin Albashi>>NLC

Kafin ya lashe zaben shugabancin kasar Amurka a 2016, sannin kowa ne cewa Donald Trump, hamshakin dan kasuwan ne kuma mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin.

Sai dai yana hawa mulki ya sauya alkibilar siyasar Amurka da ce-ce-kucen da yake yawan haifarwa da rarrabuwar-kawuna da ya haddasa ta hanyar nuna cewa shi mai kishin kasa ne.

Kalamansa a kullum cikin yanayi na fusata, kamar na bada kariya da bijiro da matakai masu tsauri da ke adawa da baki, da kuma alkawarin sake gina Amurka, sun sa masa farin jini.

Sai dai bayan rashin nasara a lokacin da ya nemi tazarce a 2020 da shan kaye a hannun Joe Biden, mutanen da suka yi imani da shi sun yar da da ikirarin da ya rinka yi a wancan lokaci cewa magudi aka yi masa na kuri’u, abin da ya kai ga sun farwa ginin majalisa a ranar 6 ga watan Janairun shekarar.

Karanta Wannan  An gano gwamnatin Tinubu na biyan Tallafin man fetur ta bayan fage duk da ikirarin da take na cewa ta cire tallafin

Tun bayan wannan lokaci Donald Trump ke fuskantar tuhume-tuhume, ciki har da na lalata da aikata Rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *