Saturday, July 20
Shadow

Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar adawa ta PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da harin da aka kai ƙauyen Ƴargoje da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Harin da ‘yan bindiga suka kai, ya kuma haɗa da garkuwa da mata da kananan yara marasa galihu, lamarin da ya kara ta’azzara wa al’ummar yankin.

Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku ya yi ƙarin haske kan harin kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron da ke amsa kiran gaggawa a kauyukan Gidan Tofa da Dan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda hudu da wasu ‘yan kungiyar sa ido na jihar Katsina guda biyu.

Karanta Wannan  Tunda ake Najeriya ba'a taba yin shugaban kasa me karfin Gwiwa kamar ni ba, na yi abinda shuwagabannin baya suka ji tsoron yi, watau cire tallafin man fetur ba tare da tunanin sake zabe na ba>>Tinubu

“Wannan babban rashi ne, kuma tunanina yana tare da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu,” in ji shi

Atiku ya soki matakan da gwamnati ke dauka kan matsalar tsaro da ake fama da ita, inda ya nuna cewa ayyukan ‘yan fashi da ta’addanci sun zama ruwan dare gama gari.

Ya bayyana damuwarsa kan gazawar gwamnati da kuma rashin ɗaukar ƙwararan matakai, duk da gagarumin kasafin kudin shekara da ake warewa tsaro.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga gwamnati da ta kara daukar nauyinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da muhimmanci.

Ya bukaci da a dauki kwararan matakai na yaƙi da matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a yankin.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Yanda 'yan B0k0 Hqrqm suka yanka mutane 7 a Bassa da Erena dake jihar Naija

“Ya kamata lafiyar al’ummarmu ta kasance a gaba, kuma dole ne gwamnati ta kara himma wajen tabbatar da hakan,” in ji Atiku

Atiku ya kuma bayyana juyayinsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, inda ya bukace su da su kara kaimi a wannan mawuyacin lokaci.

A ranar Lahadin da ta gabata ne mazauna garin Yargoje suka faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa maharan sun afka wa ƙauyen tun da dare inda aƙalla mutum 50 aka kashe sannan aka sace wasu da ba a san adadinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *