Monday, December 16
Shadow

Kalli Bidiyo da hotuna yanda motar Dangote ta buge mutane 3 suka mùtù a Jihar Legas

Hukumar kula da ababen hawa ta jihar Legas, LASTMA ta tabbatar da mutuwar mutane 3 bayan da motar Dangote ta bugesu.

Rahoton Daily Post yace motar Dangoten dake tafiya akan titin Ita-Opo, Epe ta samu matsalar birki ne inda hakan yasa ta yi taho mu gama da wasu motocin.

Shugaban hukumar ta LASTMA, Olalekan Bakare-Oki ya tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakin hukumar Taofiq Adebayo, yace motar ta Dangote ta buge Keke Napep da wata mota dake ajiye a gefe.

Karanta Wannan  Sheikh Alkashnawy Ya Kammala Karatun Digirinsa Na Biyu Da Sakamako Mafi Daraja A Jami'ar Annadha Dake Ƙasar Niger

Yace direban keke Napep din da dalibai biyu daga makarantar Manpower Technical School sun mutu sanadiyyar hadarin

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon wasu na rokon Kabarin Shehu ya kawowa Najeriya saukin tsadar man fetur ya dauki hankula

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *