Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja daga kasar Saudiyya inda ya je wajan taron kasashen Musulmai.
Jirgin na shugaba Tinubu ya sauka ne da misalin karfe 8 na darennan a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International airport.
Manyan jami’an gwamnati ne suka mai maraba bayan saukarsa.