Wani dan kasar China a birnin Legas ya wulakanta takardar Naira saboda hukumomi a jihar ta Legas sun kulle kamfaninsa saboda karya wasu dokoki.
Lamarin dai ya farune a kan hanyar Lekki-Epe expressway.
Tuni dai Bidiyon ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda da dama ke kiran ya kamata a hukuntashi.