Rahotanni sun bayyana cewa matatar man fetur ta Aliko Dangote ta ci gaba da siyo man fetur daga kasar waje bayan kwashe watanni 3 ba tare da yin hakan ba.
Hakan ya fito ne daga jaridar Bloomberg Inda tace yanzu haka akwai jiragen ruwa biyu dauke da man fetur din sun taso daga kasar Amurka zuwa Najeriya matatar ta Dangote.
Hakan na zuwane bayan da aka yi maganar cewa kamfanonin dake hako man fetur a Najeriya zasu rika sayarwa da Dangoten danyen man fetur da kudin Naira maimakon dalar Amurka.
Saidai wannan sabon labari na alamta cewa ga dukkan alamu wannan yarjejeniya ta samu Matsala.