Monday, December 9
Shadow

Abubuwan dake kawo ciwon mara

Abubuwa da yawa na kawo ciwon Mara. Masana ilimin kiwon lafiya sun bayyana cewa yawancin ciwon Mara yana samo asaline daga abubuwan cikin jikin mutum dake daidai mararsa.

Ga jadawalin Abubuwan dake kawo ciwon Mara kamar haka:

  1. Kananan Hanji.
  2. Mafitsara
  3. Babban Hanji.
  4. Appendix.
  5. Ovaries ko ace ma’ajiyar kwayayen haihuwa na mata.
  6. Mahaifa.
  7. Mafitsara.
  8. Bladder ko ace majiyar fitsari.
  9. Sannan akwai wani abu da ake cewa Peritoneum Wanda ke baibaye da kayan cikin mutum yake taimaka musu wajan yin aiki yanda ya kamata.

Duka wadannan abubuwa idan suna ciwo, mutum zai iya jin ciwon a mararsa.

Hakanan koda Idan tana ciwo, zata iya harbawa Mara, suma golaye ko ‘yayan maraina idan suna ciwo, zasu iya harbawa Mara.

Karanta Wannan  Meke kawo ciwon mara lokacin al ada

Hakanan infection da gyambon ciki Wanda make kira da ulcer ma na iya kawo ciwon Mara.

Ba za’a iya Sanin ainahin menene matsalar dake damun mutum ba kawai Dan yace yana jin ciwon maraba, idan ciwon Mara yayi tsanani ko yana yawan zuwa akai-akai, a tuntubi likita.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *