Monday, December 16
Shadow

Gyaran fuska da alkama

Alkama na daya daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajan gyaran fuska.

Ga wasu daga cikin abubuwan da alkama ke yiwa fuska kamar haka:

Alkama na kawar da tattarewar fuska.

Tana sa hasken fuska.

Tana maganin kurajen fuska da dark spot.

Tana kawar da duhun fuska da hasken rana ke kawowa.

Tana sanya fuska ta rika sheki da daukar ido.

Ga masu yawan mai a fuska, Alkama na daidaitashi.

Ana iya niko Alkama a yi amfani da garin ko kuma a yi amfani da fulawa duka za’a samu sakamako iri daya.

Yanda ake amfani da Alkama dan gyaran fuska

Ana iya kwaba garin Alkama ko fulawa da ruwa kawai a shafa a fuska a barshi yayi mintuna 15 zuwa 20 sai a wanke da ruwan dumi.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da manja

Ana kuma iya hada Fulawar ko garin Alkamar da madara a kwaba a shafa a fuska dan samun karin samako me kyau.

Ana kuma hada garin fulawa ko Alkama da kurkur da lemun tsami a kwaba a shafa a fuskar, Ana yin wannan hadi ne musamman idan anason fuska ta yi hasken irin na bleaching.

Ana saka fulawarne da yawa, kamar babban cokali 2.

sai a saka kurkur din kadan, sannan a diga ruwan lemun tsami ba da yawa ba.

Sai a kwaba a shafa a fuska a bari yayi mintuna 15 zuwa 20 sannan a wanke da ruwan dumi.

Idan ba’a son fuskar ta yi haske sosai, ta yanda za’a gane an yi bleaching, to sai a lura idan fuskar ta fara yin haske daidai yanda ake so, sai a daina shafawa.

Karanta Wannan  Gyaran gashi da aloe vera

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *