Monday, December 16
Shadow

Meke kawo kaikayin kan nono

Kaikayin kan mono abune da mata da yawa kan yi korafi akanshi.

Abubuwa da yawa na kawo kaikayin kan nono, wasu daga cikinsu sune:

Shayarwa: Mace me shayarwa na iya yin fama da kaikayin kan nono kamar yanda masana kiwon lafiya suka tabbatar.

Bushewar Fata: Macen dake bari fatar jikinta musamman nononta na bushewa, Zata iya yin fama da kaikayin kan nono.

Cutar Infection: Akwai cutar infection dake kama kan nono ya yi ta miki kaikai, shima hakan na kawo kaikan kan mono.

Mace me ciki da me jinin al’ada da wadda ta fara manyanta duk zasu iya yin fama da kaikayin kan nono.

Karanta Wannan  Meke kawo ruwan nono ga budurwa

Wadda akawa aiki a nononta itama zata iya yin fama da kaikayin mono.

Kalar sabulun wankanki ko omo da kike amfani dashi duk zasu iya kawo kaikayin kan nono.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *