Thursday, October 3
Shadow

Gyaran nono da makilin

Ki nemi:-
1-man kadanya
2-man wanke baki(makilin)

Za ki tautausa gefen nononki na kamar minti goma hakan yana bawa jijiyoyin jini damar kawo sinadarin (estrogen wanda yake sa nono girma, sai ki shafa man kadanyar a nonon ki shafa sosai daga sama zuwa kasa ta gefe yadda zai samu damar shiga fatar, sai ki sa man wanke bakin wato makilin akan tsinin nonon, in gari ya waye da safe sai ki wanke.
Za ki Yi mamaki cikin sati biyu Insha Allah.

DON MATAN AURE DA ‘YAMMATA
GYARAN NONO!

Nono! (Breast) wani bangare ne mai matukar muhimmanci a jikin ‘ya mace wanda ke kara mata kwarjini,kima da kuma ado ba ga namiji ba kad’ai harma a cikin ‘yan uwanta mata,nono ya kasance wani guri da yafi ko ina jan hankalin tare da tayar da sha,awar da namiji a jikin mace.
Binciken masana ya nuna cewa nono na iya kai har shekara 40 bai zube ba in ya samu cikakkiyar kulawa, amma abin takaici ne yadda za ka ga wani ko shekara biyar ba ya yi sai ya zube sakamakon rashin sanin darajarsa da kuma sakaciirin na wasu matan, inda za ka ga wata tun kafin su yi aure ya koma kamar silifad, in za ta fita sai dai a daure shi da dankwali sannan a tallafe shi da bireziya, wanda hakan na haifar da matsala bayan aure, don kuwa shi ango tunaninsa tulu ya saya sai an zo gida sai ya ga silifas. Abu ne sananne kuwa cewa wajen matan aure ya kan rage darajarki da janhankalin maigida inda hakan kan sa shi kallon masu tsayayyu tare da sha’awar kara aure. Don haka ya zama wajibi a wajenki ki kula da nonuwanki sosai domin shayarwa bata zubar da nono in kin iya kula dashi.

Karanta Wannan  Gyaran nono a sati daya

Sannan Kuma sanin kalar shape din nononki nada tasiri wajen sanin bireziyar da ya kamata ki saya domin gujewa zubewarsu.

DALILAN DAKESA NONOWA ZUBEWA:-

1-rashin amfani da bireziya
2-sa kaya damammu marasa breastcurve
3-daurin qirji
4-fito da nono ta saman riga ko bireziya
5-shan taba sigari
6-rashin cin abinci mai gina jiki
7-yawan tsalle-tsalle
8-yawan wanka da ruwan sanyi.
sai a kiyaye
YADDA ZA AI GYARA:-

               1-CIKOWAR NONUWA

Wannan hadin mace tana yin shi domin nonuwanta su girma tare da cikowarsu.
Abubuwan da za ki nema:
1-Jar masara
2-Farar shinkafa
3-Alkama
4-Gero
5-nono kindirmo
zaki hada jar masara, farar shinkafa,alkama da kuma gero a niko su banda surfawa sai ki tankade,ki dinga shan cokali 4 bayan abinci dare da kindirmon nonon

Karanta Wannan  Gyaran nono lokacin yaye

2-DONKARIN GIRMA DA HANASU ZUBEWA

1-aloevera gel
2-kwai
3-kokonba

Wannan Kuma za ki samu aloevera ki yanke fatocin saman ki kwashe abun cikin wato gel,saiki fasa kwanki ki kwashe farin ruwan banda kwanduwa,saiki markada kokonbarki ki tace ruwan,ruwan dashi za kiyi amfani,ki hadesu duka, ki dinga shafawa da daddare kafin barci da safe ki wanke da ruwan dimi,ki sami original vasilline wanda aka rubuta vasilline a jiki, ki fara tautausa gefensu kamar na minti 5 sai ki dauki kamar minti biyar kina shafa masu. Za ki Yi matukar mamaki cikin sati biyu ko uku insha Allahu

                  3-GIRMAN NONO

Shi Kuma Wannan hadin ana bukatar abubuwa kamar haka:-

Karanta Wannan  Meke kawo ruwan nono ga budurwa

1-habbatul sauda
2-hulba
3-shinkafa
4-madara

Za ki hade su guri guda ki dinga kununsu kina sha awa biyu kafin bacci, na sati biyu xuwa sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *