Wednesday, April 8
Shadow

Isra’ila ta lalata asibiti na ƙarshe a arewacin Gaza – WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sojojin Isra’ila sun lalata babbar cibiyar lafiya ta ƙarshe da ta rage a arewacin Gaza.

WHO ta ce rahotanni sun bayyana cewa an ƙona wasu muhimman sassa da aka lalata a harin da aka kai ranar Juma’a a asibitin Kamal Adwan.

Hukumar ta kuma nuna matuƙar damuwa game da lafiyar majinyatan da aka tilasta musu barin asibitin.

Isra’ila dai ta ce Hamas na amfani da asibitin ne a matsayin cibiyar ba da umarni – amma ba ta gabatar da wasu hujjojin da ke gaskanta hakan ba.

Karanta Wannan  Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *