Friday, December 12
Shadow

Hotuna: An kama ma’aikaciyar Gidan yari na lalata da me laifi

Hukukomin Gidan yari a kasar Ingila sun kama wata ma’aikaciya da bidiyonta ya bayyana tana lalata da me laifi.

Jaridar TheSun ta ruwaito cewa, an kama ma’aikaciyar me shekaru 19 ne bayan da bidiyon lalatar da ta yi da me laifi a gidan yarin ya watsu sosai.

An rika aikawa mutanen dake aiki a gida yarin bidiyon dama sauran wanda ke waje har ta kai ga ya kai ga hukumomin gidan yarin.

A kasar ta Ingila dai ana yawan samun irin wannan matsala inda mata ma’aikatan gidan yari kan yi lalata da mazan da ake tsare dasu.

A baya an kori mata kusan 29 saboda irin wannan halayya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Dan Gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Ibrahim El-Rufai, sanye da Dan Kunne, Yayi Kitso, sannan yace yana saka Sarqa da Barimar hanci ya dauki hankulan mutane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *