Saturday, January 4
Shadow

NNPCL ya ce matatar mai ta Warri ta koma aiki

Kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPCL ya ce matatar mai ta garin Warri na jihar Delta ta ci gaba da aiki.

Shugaban NNPCL Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a matatar mai ƙarfin tace gangar mai 125,000 a kullum.

“Duk da cewa ba 100 bisa 100 take aiki ba, muna kan aikin gyaran,” in ji shi yayin da shugaban hukumar kula da harkokin mai na kamfanin Farouk Ahmed ke yi masa rakiya.

“Mutane da yawa na tunanin yunƙurin namu ba gaskiya ba ne. Suna tunanin ba zai yiwu a aiwatar da abubuwa na ƙwarai a Najeriya ba, amma muna so ku gani da idonku.”

Karanta Wannan  Ga Bashi daga Gwamnatin Tarayya: Zaka iya neman daga Naira Miliyan 3 zuwa 20

Matatar da ke yankin Ekpan na Warri, an ƙaddamar da ita a shekarar 1978 domin samar da mai ga jihohin kudancin Najeriya bisa kulawar kamfanin NNPCL .

A cewar mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye, an tsara kammala aikin ne tun cikin wata ukun farko na 2024.

A watan Nuwamban da ya gabata ne NNPCL ya ce ya kammala gyaran tsohuwar matatar mai ta Fatakwal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *