Wednesday, January 8
Shadow

Jaruman Kannywood da suka rasu a 2024

Har yanzu masana’antar Kannywood da masu bibiyarta suna tunawa tare da jimamin rasuwar fitaccen mawaƙi El’mu’az Birniwa, wanda ya rasu a daren Laraba, 4 ga Disamban 2024 a Kaduna.

Irin yanayin da mawaƙin ya yi rasuwar fuju’a ce ta sa jimaminsa da ake yi ya ɗauki lokaci, kamar yadda ake yi idan an yi mutuwar farat-ɗaya.

Mawaƙi El-Mu’aza ya shiga sahun irin su Saratu Daso da Mustapha Waye da darakta Aminu S. Bono wajen yin irin rasuwar ta fuju’a.

A daidai wannan lokaci da muka yi ban-kwana da shekarar 2024, BBC ta tattaro wasu ƴan masana’antar da suka bar duniya a shekarar.

Fatima Sa’id (Bintu)

A ranar Lahadi 11 ga Fabrairun 2024 ne Allah ya yi wa jaruma Fatima Sa’id, wadda aka fi sani da Bintu Dadin Kowa rasuwa.

Karanta Wannan  Yadda Gwamnan Kano, Abba Kabir Ya Jagoranci Duba Lafiyar Yaran Da Aka Sako A Asibiti, Bayan Kyakkyawar Kulawar Da Suke Samu Ta Bangaren Abinci Tun Bayan Da Suka Dawo Kano

Jarumar wadda ta fi yin fice a shirin na tashar Arewa24 ta rasu ne sakamakon rashin lafiya.

Da dama daga cikin abokan aikinta sun bayyana ta a matsayin mai natsuwa, wadda ba ta da hayaniya.

Saratu Giɗaɗo

Ita kuma Saratu Giɗaɗo, wadda aka fi sani da Saratu Daso, ta rasu ne a ranar Laraba 9 ga watan Afrilun 2024.

Jarumar ta rasu ne bayan ta kammala shirye-shiryen sallah, kuma an yi sahur da ita, amma aka wayi gari ta rasu.

Mutuwar fuju’a da Hajiya Saratu ta yi ya girgiza masana’antar ta Kannywood da ma duk maau kallon fina-finan Hausa a duniya.

Za a tuna tauraruwar da taka rawa babu tsoro ko shakku a finafinai, sai kuma barkwancinta.

Tana daga cikin mutane masu yawan tsokaci a kan duk wani abu da BBC Hausa ta wallafa a shafukan sada zumunta.

Karanta Wannan  Yanzu Mace Ba Allura Bace A Cikin Ruwa, Mangoro Ce Akan Faranti Sai Wadda Kake So, Cewar Ummi Ibrahim

Fati Usman

A watan Mayun 2024 ne aka samu labarin rasuwar tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood, Fatima Usman, wadda aka fi sani da Fati Slow Motion.

Fati ta rasu ne a yankin Ouaddai da ƙasar Chadi, kuma a can aka binne ta.

‘Yan’uwanta sun shaida wa BBC cewa ta rasu ne bayan jinyar ‘yan kwanaki.

Duk da cewa a lokacin rasuwarta ba ta yawan fitowa a finafinai, amma tana daga cikin wadanda suka yi tashe a shekarun farko-farko na habbakar masana’antar Kannywood.

Sannan a baya-bayan nan ta rika tashe a shafukan sada zumunta, inda ta bar wa mutane sarar amfani da kalmar ‘kebura’.

Sulaiman Alaqa

Sulaiman Alaqa jarumin Kannywood ne da ya rasu ne a ranar 22 ga watan Yuli 2024.

Shi ne mahaifin jaruma Bintalo ta Dadin Kowa.

Karanta Wannan  Kalli Kayatattun hotunan Fati Washa

Ya dade yana taka rawa a masana’antar Kannywood tun yana matashi.

Duk da cewa tauraruwarsa ba ta haska kamar ta wasu daga cikin jaruman da suka taso tare ba amma ya bayar da gudumawa sosai a masana’antar.

El-Muaz Muhammad Birniwa

A daren ranar Laraba, 4 ga watan Disamban ne Allah ya yi mawaƙi El-Mu’az Birniwa ya rasu.

A tattaunawarsa da BBC, Birniwa, wanda dan asalin jihar Jigawa ne amma aka haifa kuma ya yi rayuwa a jihar Kaduna, ya ce babban abin da ke bata masa rai shi ne rashin cika alkawari.

Kamar Saratu Gidado, rasuwar fuju’a da El-Muaz ya yi ta sosa ran ‘yan masana’antar Kannywood da ma sauran masu mu’amala da masana’antar.

Ya rasu ne yayin da ake shagulgulan taya abokin aikinsa, Auta Waziri murnar aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *