Abubuwan dake haddasa Karyewar gashi sun hada da yawan damuwa, zafi, ciwo me tsanani irin su ciwon suga, hawan jini da sauransu.
A wannan rubutu zamu yi cikakken bayani game da karyewar gashi da maganin hana karyewar gashi.
Bushewar gashi da barinshi ba gyara ma yana sawa ya rika kakkaryewa.
Ga cikakken bayani kamar haka game da abubuwan dake kawo karayar gashi:
Abinci: Kalar abincin da ake ci na taimakawa matuka wajan kyawun gashi da kuma hana karyewarsa. Kalar abincin dake taimakawa wajan hana karyewar gashi sune, dafaffen kwai, gasashshiyar kaza, ganye irin su kabeji, dodon kodi, madara, da Yegot.
Yawan Damuwa: Kasancewa cikin yawan damuwa na sanya karyewar gashi. Dan haka, masana sun bada shawarar a rika cire kai daga cikin damuwa dan samun gashi me kyau da baya karyewa.
Bushewa: Barin gashi ya bushe sosai yana sanya ya rika bushewa. Hakanan zafi sosai shima yana sanya gashi ya rika karyewa, dan haka ko da wanke gashin za’a yi, kada a yi amfani da ruwan zafi, a yi amfani da ruwan dumi.
Yawan Gyaran Gashi: Yawan gyaran gashi akai-akai yana sa gashi ya rika karyewa. Masana gyaran gashi sun bada shawarar cewa, a rika bada tazarar akalla kwanaki 8 zuwa 10 kamin sake yin gyaran gashi.
Busar da gashi da tawul: Bayan kammala wanke gashi ko bayan wanka, amfani da tawul a rika gurzawa na karya gashi. Abinda yafi shine a nade gashin da tawul din a barshi ya tsane.
Sharce Gashi ba daidaiba: Yawan sharce gashi akai-akai yana kawo karyewar gashi. A shawarce ya kamata sai an wanke gashine kamin a sharce, sannan kada a sharce gashin yana jike, a bari ya bushe, sannan a yi amfani da comb ko masharci me wara-wara.
Idan aka kiyaye wannan abubuwa, insha Allahu za’a samu warwarewar matsalar karyewar gashi.