Friday, January 10
Shadow

Bayyana Kyautar Motar Da Yara ‘Ýan Maťàñ Nan Śuke Yì, Ya Fi Illa Fiye Da Àbìnda Suke Źuwa Ýi Ake Ba Šu Motar

Daga Jamila Ibrahim

Ni Wallahi yaran nan da ake bawa mota fitowa da suke yi suna nunawa ya fi illa akan abinda suke zuwa ýi ake ba su.

Yanzu sun yi influencing yara kanana na ťìķțok har ya kai ga burin yarinya kawai ta yi ìşķançì a ba ta kudi, yara sun fara fandarewa.

In an basu suyi hakuri su daina zuwa suna posting don yadawa duniya.

Ku kuma ‘yan mata da kuke kallon wadanda ake bawa gida da mota as role model har suke burge ku ku sani ba haka kawai ake ba su kudin ba, wani abun ya wuce kudin da saurayi zai bawa budurwa sabida soyayya ko sabida ya yi źìñà da ita, yawanci kudin ķùñģiya ce, bayan wasu shekaru za a a nemi wadanan dukiyar a rasa ka zama abun tausayi.

Karanta Wannan  An kama wata budurwa bayan da saurayi ya kashe mata makudan kudade amma tace ba zata aureshi ba

Zan iya misalai da ‘yan fim dayawa wadnda ma suka tare kasar waje suka yi suna, suka yi kudi amma karshen su yanzu bai yi kyau ba.

Ku zauna inda Allah ya ajiye ku ku ci kudinku na halal, suna zuwa social media ne suna fada an basu don su sami karin mutane da za su tagayyara tare.

Don Allah don Annabi ku yi hakuri da talaucin ku, ku kare mutuncinku da na iyayenku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *