Friday, December 5
Shadow

An kubutar da yara 4 da aka sace daga jihar Bauchi aka kaisu Jihar Anambra aka sayar

Hukumar ‘yansanda a jihar Anambra ta sanar da kubutar da wasu yara 4 da aka sato daga jihar Bauchi aka kaisu Anambra aka sayar dasu ga wasu iyalai.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, Obono Itam ne ya bayyana haka inda yace sun kama mutane 4 da ake zargi da hannu a lamarin.

Ya hayyana hakane ranar Litinin, 6 ga watan Janairu inda yake bayani game da yanda hukumar tasa ta gudanar da ayyukanta a shekarar 2024.

Yace daya daga cikin yaran an ganeshi kuma dukansu za’a mayar dasu ga iyayensu.

Ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun amsa laifukansu.

Karanta Wannan  Barawo Ya Sace Wayar Wannan Malamain, Bayan Kwana Biyu Kuma Barawon Ya Mutu, Shine Ake Zargin Malamain Da Hannu A Mutuwar Barawon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *