Saturday, January 11
Shadow

Ya kamata a hukunta Alkalin da yace sake nada Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba daidai bane>>Inji El-Rufai

Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bukaci cewa ya kamata a hukunta Alkalin babbar kotu tarayya da yayi hukuncin cewa sake nada me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin sarki baya kan ka’ida.

El-Rufai wanda abokin Sarki Sanusi II ne ya bayyana hakane a ta shafinsa na sada zumunta inda yake taya Sanusi II murnar tabbatar dashi a matsayin sarkin Kano da kotun daukaka kara tayi.

A baya dai Kotun tarayya ta yi hukuncin cewa, sake nada Sarki Sanusi II baya kan doka amma a yanzu kotun daukaka kara ta soke wancan hukunci.

El-Rufai ya kara da cewa, babbar kotun tarayya bata da hurumin shiga maganar masarauta wadda bata cikin garin Abuja.

Karanta Wannan  Gwamnoni sun kai ziyarar jaje zuwa Maiduguri

An ga dai yanda masoya sarki Sanusi II suka barke da murna bayan da aka tabbatar dashi a matsayin sarkin Kanon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *