Kwamitin Majalisar dattijai dake saka ido kan yanda ake kashe kudaden gwamnati ya nemi ministan kudi, Wale Edun yayi bayani kan yanda aka kashe kudin tallafin man fetur da aka cire.
Saidai Wale yace wannan magana ta sirri ce, dan haka ne kwamitin suka kori ‘yan majalisa daga zaman dan Wale ya musu bayani.
Wannan magana ta taso ne bayan da sanata Senator Abdul Ningi dan PDP daga jihar Bauchi ya bukaci hakan.
Shugaban kwamitin, Senator Olamilekan Adeola ya nemi ‘yan jarida su fita daga zaman dan a samu a yi maganar yanda aka kashe kudin tallafin man fetur da aka cire.
Gwamnatin tarayya dai tace ta cire tallafin man fetur ne dan amfani da kudaden wajan yin ayyukan raya kasa.