Saturday, January 11
Shadow

Duk da ciyo bashin Dala Biliyan $3.2 Najeriya ta kasa samar da ingantacciyar wutar Lantarki

A cikin shekaru 4 da suka gabata, Najeriya ta ciyo bashin Dala Biliyan $3.2 dan gyaran wutar lantarki amma duk da haka ta kasa samar da wutar me karfin da yafi 4,500mgwt da zata wadatar da mutanen kasar.

Bankin Afrika da Bankin Duniya da Bankin Japan ne suka baiwa Najeriya wadannan kudade.

Saidai duk da wadannan makuda kudade babu alamar canji kan matsalar wutar.

Har yanzu dai wuta me karfin Megawatts 4,743MW ne Najeriya ke samarwa wanda tun shekaru 3 da suka gabata haka lamarin yake bai canja ba.

A shekarar 2024, sau 12 tashoshin wutar lantarkin Najeriya na samun matsala.

Karanta Wannan  Babban Fasto a Najeriya, Enoch Adebayo ya yi karin haske kan maganar cewa ya musulunta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *