Sunday, January 12
Shadow

Gwanin Ban Tausai: Ji yanda kananan ‘yan matan da aka yi gàrkùwà dasu aka sakosu suka koma yin karuwanci saboda ‘yan Bìndìgàr sun saba musu da làlàtà

Lawan Wakilbe, kwamishinan ilimi, da kimiyya da fasaha, da kirkire-kirkire a Jihar Borno, ya yi gargadi kan yawaitar karuwanci tsakanin tsofaffin wadanda kungiyar B0k0 Hàràm ta sace.

TheCable ta rawaito cewa Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da Hamsatu Allamin, shugabar cibiyar Allamin Foundation for Peace, ta kai masa a jiya Juma’a a Maiduguri.

Wakilbe ya ce an fi samun irin waɗannan matsalolin a ƙananan hukumomin Bama, Banki, da Gwoza.

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda Boko Haram din su ka saki na fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata da su saboda sun fuskanci hakan tun a lokacin da raunin da su ke hannun ƴan ta’addan.

Karanta Wannan  Zamu fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci>>Gwamnatin Tarayya

Ya yi kira ga haɗa hannu waje ɗaya domin ceto ire-iren yaran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *