Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar su tsohon Gwamnan Kano kuma sanata Ibrahim Shekaru me suna LND dake son rikidewa zuwa ta siyasa, ta samu goyon bayan tsaffin shuwagabannin Najeriya, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo.
Kungiyar dai na ci gaba da tuntubar manyan ‘yan siyasa dga yankunan Kudu maso yamma da kudu maso kudu da kudu maso gabas dan cimma burinta.
Shugaban kungiyar, Dr Umar Ardo ya tabbatar da komawarta ta siyasa dan samar da Jam’iyya me karfi da hadin kai da zata karade kowane yanki a kasarnan.
Duka shuwagabannin biyu, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo sun yi na’am da wannan tafiya inda suka bayar da shawarar mayar da ita ta kasa baki daya.