Friday, December 5
Shadow

A yayin da Gobarar California kasar Amurka ke ci gaba da yaduwa, an hango wata mahaukaciyar Guguwa ta taho zata rura wutar ta kara shiga cikin gari dan ci gaba da kona gidaje

Wata mahaukaciyar guguwa da aka sakawa sunan Santa Ana winds dake gudun mita 45 duk awa ta doso garin Los Angeles dake ci da wuta.

Ana tsammanin wannan guguwa zata rura wutar inda zata turata zuwa sassan garin dake da muhimmanci kamar gidan tarihin garin me suna J. Paul Getty Museum da kuma jami’ar University of California.

Tuni dai aka fitar da sanarwa ga mutanen dake yankin da su fice daga gidajensu.

Zuwa yanzu dai gobarar ta kone sama da gidaje dubu goma sha biyu da kuma yin sanadin kisan mutane 16 inda mutane 13 sun bace ba’a san inda suke ba.

Karanta Wannan  Ashe Maganar Juyin Mulki Gaskiya ce, shiyasa naga manyan kasar Hadda Tinubu sun tafi kasashen waje ta yanda idan an yi juyin Mulkin zasu samu sauki>>Inji Tsohuwar Hadimar Shugaban kasa, Lauretta Onochie

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *