Innalillahi Wa Inna Ilaihir Rajiun
Wani Mutum ya rasu yau a Abuja a hotel lokacin da suke aikata zina shida budurwar sa da suka hadu a social media
Bincike ya tabbatar da cewa Ƙwayoyin kara karfin maza ne yayi sanadiyar mutuwar tasa, ita budurwar tasa ƴar jahar Jigawa ce Ƙaramar Hukumar Dutse, tayi karya taje har Abuja ta same shi
Allah ya tsare mu da mummunar kaddara.
Cikakken Bayani:
MARYAM TA JE ABUJA KARBAN iPhone 16 KO? LISSAFI YA KWABE!, DARASIN RAYUWA!
Dazu da safe, Manajan gidan hotel na Palasa dake yankin Gwagwalada Abuja ya kai kara ofishin ‘yan sanda na Gwagwalada bayan wani mutum ya mutu a dakin hotel din da ya kama shi da wata karuwa
Sunan wanda ya mutu Lawal Ibrahim, sunan karuwarsa kuma Maryam Abba daga birnin Dutsen Jihar Jigawa, wanda sun hadu a social media watanni uku da suka wuce
Abinda ya faru shine, Lawal ya kira Maryam zuwa Abuja, jiya da dare ya sauketa a Palasa Hotel sukayi zina, da garin yau Laraba ya waye da misalin karfe 6 na safe suka sake yin zina, Maryam tace suna cikin yin zina ya fado daga kanta ya suma numfashinsa ya dauke, ta yayyafa masa ruwa bai farfado ba
Shine sai ta sanar da ma’aikatan gidan hotel din akazo aka daukeshi aka kai asibiti inda Likita ya tabbatar da Lawal Ibrahim ya mutu.
A yanzu haka Maryam tana hannun ‘yan sanda an kaita zuwa Force CID Abuja don tabbatar da bincike akan musabbabin mutuwar abokin fasikancinta, abubuwa da aka samu sun hada da kankana da miyagun kwayoyi masu kara karfin jima’i
Darasin da zamu dauka anan shine:
Maryam ‘yar Jihar Jigawa ne daga birnin Dutse, ta yiwa iyayenta karya ta taho Abuja domin ayi lalata da ita, abokin lalata ya mutu a kanta lokacin da suke cikin yin fasikanci, Allah ne Kadai ya san ranar da zata kubuta daga wannan tuhuma na kisan kai da ake mata
Mutane mu ji tsoron Allah, babu wanda ya san a wani irin yanayi ajali zai zo masa, tabbas akwai abin takaici ace mutum musulmi yayi mummunan karshe irin wannan
Matansa da ‘ya’yansa da iyayensa, da ‘yan uwa da abokansa duk sai sun yi da na sanin saninsa a rayuwa
Haka ita ma yanzu Maryam sai tayi nadamar zuwanta duniya, domin yanzu lissafi ya kwabe mata, iyayenta da ‘yan uwanta da sauran samarinta da take yaudara duk zasu san halin da take ciki
Don Allah mu yi iya bakin kokarinmu wajen aikata ayyukan alheri tare da gudun munanan abubuwa da zasu rusa mana tarihi su zubar da kima da mutuncin mu
Allah Ya tsare mana imanin mu, Ya bamu karfin yakar shaidan
Shi kuma Lawal Ibrahim Allah Ya yafe masa, Ya bashi Aljannah don rahamarSa