Bankin Duniya ya bayyana cewa, tattalin arzikin Najeriya zai karu da kaso 3.6 tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026.
Bankin yace hakan zai farune bayan da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta dauki matakan tada komadar tattalin arziki.
Bankin yace bangarorin da suka fi samun tagomashi sune na kudi da kuma sadarwa.
Matakan da gwamatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta dauka sun hada da cire tallafin man fetur da karya darajar Naira da sauransu.