Friday, January 17
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta ware N252.89bn dan ci gaba da gyaran titin Abuja zuwa Kano tace cikin watanni 12 za’a kammalashi

Gwamnatin ta sanar da amincewa da fitar da Naira N252.89bn dan ci gaba da gyaran titin Abuja zuwa Kano.

Ministan Ayyuka, Dave Umahi ne ya tabbatar da hakan inda yace za’a gabatar da wannan magana a gaban majalisar zartaswa ta kasa dan amincewa da ita.

Kamfanin da aka baiwa kwangilar wannan aiki shine Infoust Nigeria Limited.

Ministan yace za’a yi amfani da fasahar zamani dan gyaran titin wanda ke saukaka tafiye-tafiye da cinikayya tsakanin kudu da Arewa.

Karanta Wannan  Kotu ta hana CBN baiwa jihar Rivers rabonta na kudaden shiga daga gwamnatin tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *