Gwamnatin tarayya tace an saka sana’o’in Aski, Gyaran waya, gyaran fanfo, kwalliyar mata, Gyaran waya da sauransu cikin abubuwan da za’a rika koyarwa a makarantun boko.
Za’a rika koyar da wadannan sana’o’i ne a makarantun firamare zuwa makarantun karamar sakandare.
Wannan ya biyo bayan garambawul da akawa bangaren ilimi.
Hukumar wayar da kai ta kasa, NOA ta ce an saka wadannan sana’o’i cikin karatu ne dan koyawa dalibai hanyar dogaro da kai.
Sauran sana’o’in da za’a rika koyarwa sun hada da noma, kiwon kaji, gini, saka tayil, saka POP, da dai sauransu.