Friday, December 5
Shadow

A 2027, Ina Da Tabbacin Cewa Kafin 12 Na Rana Tinubu Ya Lashe Shugaban Kasa, Cewar Nazir Ɗanhajiya

ZABEN 2027: Ina Da Tabbacin Cewa Kafin 12 Na Rana Tinubu Ya Lashe Shugaban Kasa, Cewar Nazir Ɗanhajiya.

Shugaban ƙungiyar wayar da kan matasa reshen Jihar Kano kuma Fitaccen Furodusan a masana’antar Kannywood, Nazir Ɗanhajiya ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa kafin 12 na rana shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaɓensa 2027.

Ɗanhajiya, wanda ya bayyana haka ta cikin wata tattaunawarsa da Dokin Ƙarfe TV, ya ƙara da cewa kaso 90 na ƴan Najeriya masoya Tinubu ne.

“Idan ka duba za ka ga kashi 1 ne zuwa 5 ake ba wa na Data suke Furofaganda a Social Media ba wai masoya ƙasar ba ne. Mu ne muka san masu zaɓe, mu ne muke tare da masu zaɓe”. Inji shi.

Karanta Wannan  Bamu yadda da karin kudin kiran waya ba, muna kiran 'yan Najeriya su kauracewa kamfanonin sadarwa>>NLC

Nazir ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su mara wa Tinubu baya ya yi shekara 8 ɗinsa domin gyara da ci gaban da yake kawo wa. “Na tabbata idan Tinubu ya gama mulkinsa sai mun yi dama-dama ya dawo ya ci gaba”. In ji Ɗanhajiya.

Menene ra’ayinku?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *