Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban Israela, Benjamin Netanyahu ya amince da tsagaita wuta akan Falas-dinawa bayan tursasawar kasar Amurka.
Rahoton yace, Israela ta amince da tsagaita wutarne a Yau, Lahadi.
A ranar Juma’ar data gabata ne dai Shugaba Biden ya gabatar da tsarin na tsagaita wuta wanda Benjamin Netanyahu yayi watsi dashi.
Saidai a yau ya amince.
Hakanan akwai rahotannin dake cewa, itama kungiyar Hamas ta amince da tsarin, amma bata sanar da hakan a hukumance ba.
Me baiwa Benjamin Netanyahu shawara kan harkokin kasashen waje, Ophir Falk ne ya bayyana hakan inda yace ba shiri bane me kyau amma suna son kubutar da duka mutane su dake hannun Hamas shiyasa suka amince dashi.
Saidai ya nanata aniyarsu ta son ganin bayan kungiyar ta Hamas.