Saturday, December 13
Shadow

A karshe dai kasar Burkina Faso ta sako sojojin Najeriya 11 da take rike dasu bayan da jirginsu yayiwa kasar Kutse

Rahotanni daga kasar Burkina Faso na cewa, kasar ta saki sojojin Najeriya 11 da take rike dasu bisa zargin jirgin saman da suke ciki ya shiga sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba.

An saki sojojin Najeriyar ne ranar Talata.

A baya dai sojojin dake mulkin kasar ta Burkina Faso sun ce jirgin sojin Najeriya me lamba C-130 ya shiga sararin samaniyar kasarsu ba tare da izini ba.

Saidai hukumomin sojin sama na Najeriya sun ce jirgin ya samu tangarda ne shiyasa yayi saukar gaggawa a kasar ta Burkina Faso.

Karanta Wannan  Bana munafurci a siyasa>>El-Rufai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *