
Masana kimiyya sun sanar da samun gagarumar ci gaba a kokarin da suka shafe shekara da shekaru suna yi na ganin sun gano karshen kasar da muke takawa.
Masanan dai suna haka ce kamar yanda ake haka rijiya dan gano karshen kasa.
A wannan karin sun ce sun yi haka a karkashin kasa da nisanta ya kai mita 1,268, wannan ba karamin ci gaba bane lura da cewa a farko burinsu shine su yi hakar da nisanta bai wuce mita 200 ba.
Dalilin su na ci gaba da hakar shine sun ga lamarin yana da dauki ba kamar yanda suka yi tsammanin zasu sha wahala ba
Saidai har yanzu basu kai karshen kasa ba.
Kasar Amurka ce dai ke daukar nauyin wannan aiki, saidai ta dakatar da bayar da kudin gudanar da aikin wanda hakan ke barazana ga ci gaban aikin.