Wednesday, November 12
Shadow

Hankula sun tashi bayan da Masu kutse suka kwashewa mutane kudinsu a Bankin Union Bank har Naira Biliyan 9.3

Rahotanni sun ce masu kutse sun kwashewa Kwastomomi kudadensu har Naira Biliyan 9.3.

Rahoton yace bankin na ta kokarin ganin ya dawo da wadannan kudade da aka sace.

Sannan tuni aka rufe wasu asusun ajiya da ake tsammanin na da alaka da satar.

Lamarin ya farune ranar 23 ga watan Maris da ya gabata.

Bankin a ranar 2 ga watan Afrilu ya nemi kotu ta bashi damar kulle wasu asusun banki da suka ce har yanzu ana amfani dasu wajan satar kudaden.

Ba wannan ne karon farko ba, Watanni 15 da suka gabata sai da babban bankin Najeriya CBN ya rushe hukumar gudanarwar bankin kan irin wannan lamari

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Akwai wanda yace mana idan Izala Gaskiya ce kada Allah yasa ya kai shekara me zuwa, kuma baikai labari ba, kamin shekara ta zagayo ya riga mu gidan gaskiya>>Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *