Friday, December 5
Shadow

A soke zaben cike gurbi na Kano, Bamu yadda dashi ba>>Inji Jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa, bata yadda da zaben cike gurbi na Kano ba inda tace INEC ta sokeshi da gaggawa.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Felix Morka ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Asabar inda yace suna kira ga INEC ta soke zaben da gaggawa.

Yayi zargin cewa, ‘yan Bangar siyasa a Shanono da Bagwai da Ghari sun tayar da hankula sosai ta hanyar amfani da muggan makamai.

Yace masu zabe dole suka tsere inda suka sha karfin jami’an tsaron da aka kai wajan wanda hakan yasa zabe me inganci ba zai samu ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda wata Guguwa me cike da yashi ta taso ta Rufe sararin samaniyar birnin Riyadh na Saudi Arabia

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *