Friday, December 5
Shadow

A zaben 2027 ba zamu saki baki a mana abinda aka ga dama ba>>Atiku Abubakar ya bayyana shirin cin zabe na musamman da yake yi

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2027, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa zaben 2027 ba zai zama kamar sauran zabukan da aka yi a baya ba.

Yace ‘yan adawa na hadaka ta musamman dan ganin sun yi nasara akan gwamnati me ci saboda tsare-tsaren gwamnatin basu kawowa kasar ci gaba ba.

Ya bayyana hakane a Abuja ranar Talata a yayin ziyarar da wasu ‘yan masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood suka kai masa.

Kungiyar tace tana tare da Atiku a zabe me zuwa.

Wani dan siyasa daga jihar Zamfara, Dr. Aslam Aliyu ne yawa kungiyar jagora zuwa wajan Atiku.

Karanta Wannan  Dangote ya baiwa David Bird shugabancin matatar mansa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *